YADDA ZAKA RAGEWA SYMBIAN PHONE CIN CHAJI Symbian waya ce, wacce ta dauki lokaci tana cin zamaninta, wadda kuma hadda zuwan wayoyi na zamani, baisa Symbian ta ji tsoro ba, saboda tana ji da kanta. Symbian ita ce waya ta farko da aka fara kirkira mai babbar Manhaja (Operating System) sannan kuma ita ce waya mafi dadewa akasuwannin manyan waya masu babban OS, sannan kuma ita ce waya ta farko da aka fara aiki da ita wajen satar bayanai na kasashen duniya, kafin zuwan android. Masarrafai da android ta tana da kuma take da saukin mu'amala tasa, wayar ta shiga ran masu amfani da ita. Duk mai amfani da wayar Symbian zaice maka tana da kokari wajen rikon caji musammam ma, idan har yayi mu'amala da wayoyin zama ni kamar android,
1) LIGHT TIME OUT Idon kanason rajewa symbian jan chaji akan ta, to saika rage lokacin da hasken kan wayarka yake daukewa, domin wata tana zuwa a 15s ko 20s wata kuwa har 30s, to ka rage yawan second din ya dawo 5s ko 10s, cajinka zai kara kwari, domin ragewa kaje, Menu > Setting > General > Personalisation > Display > Light time-Out. Saika rage zuwa 10s ko 5s.
2. POWER SAVER TIME-OUT Haka kuma ka kara rage lokacin ''Power Saver time domin rage lokacin saika je Menu > Setting > General > Personalisation > Display > Power saver time-out ka rage ya dawo 10s ko 5s.
3. LIGHT SENSOR Ka rage hasken da screen naka yake da shi, wato ka dan sa masa duhu kadan domin, hakan zai kara baka kariya ga idonka, sannan kuma ka kara samun tattali, saboda wasu sukan sa screen guard saboda rage hasken fuska, amma kuma jan cajin wayar bai ragu ba, to amma idan ka bi wannan matakin zaka samu saukin jan caji, domin yin hakan kaje, Menu > Setting > General > Personalisation > Display > Light Sensor, saika rage kadan.
YADDA ZAKA RAGEWA SYMBIAN PHONE CIN CHAJI
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment