CIGABAN DA WAYA TA SAMAR A HANYOYIN SADARWA

Ba’a taba samun sauki wajen harkar sadarwa ba kamar yadda muka sami hanyoyin sadarwa iri iri a wannan karnin. Hakika idan muka dubi bangaren ci gaba da aka samu ta harkar waya a wajen sadarwa za mu fahimci cewa lallai sadarwar waya ta taimaka wajen saukaka aikace aikace da kuma aikawa da sakonni da makamantansu.
Ka dubi sauki da aka samu a wajen magana a ko’ina tare da Wayar-Tafi-Da-Gidanka wanda a da kamar yan shekarun baya ko ita kanta waya ana amfani da tangarahone wacce sai dai kaje jikin bango ko kuma wani sako da aka ajiyeta kaje ka amsa wayar. Amma idan muka duba Wayar-Tafi-Da-Gidanka zaka ga cewa abin ya zamanto mafi sauki matuka yadda a da sai dai ka sami layi guda tal a gida guda ko da kuwa akwai kowanne tangaraho da yawa. Amma a wannan lokaci zaka samu cewar a gida guda sai a sami kawunan wayoyi da layika daban daban wanda idan aka sami gida guda tare da samari kamar goma sai ka samu dukkansu sunada waya kusan kowanne da hanyar wayar da yake amfani da shi fiye da daya.
Ana amfani da Wayar-Tafi-Da-Gidanka wurin ajiye ajiye kama daga ajiye hotuna, hoto mai motsi, sauti kamar karatuttuka, wakoki da dai makamantansu.
Idan kuma muka duba ci gaba da wayar celula ko kuma Wayar-Tafi-Da-Gidanka ta kawo ta fannin saukaka sadarwa zamu iya danganta shi da nasara mai yawa, kama daga yadda muke so mu rinka magana da abokan huldan mu, ko kuma dangi, zamu ga cewa lallai waya ta saukaka, idan kuma ta zo bangaran sakon karamin wasika shine zamu ga yadda waya ta bada sauki wajen aikawa da rubutaccen sako (SMS) sa’annan kuma ga sako wanda yafi karamin rubutu wanda ake kira da MMS wato (multimedia message)wanda zaka sami cewar zaka iya daukar sauti, ko karatu ko waka, ka aika da ita zuwa ga abokin hulda kamar yadda kake aika wa da karamin sako. Kamar yadda kake iya aika wa da sauti (Audio) haka zaka iya aika wa da hotuna da kuma hoto mai motsi (Video), wanda awancan lokacin na baya idan kace hakan zai faru ta harkar sadarwa ko ni mai rubutu zan karyataka.
Ba ta wannan kadai bane hanyar sadarwa ta kawo ci gaba ta amfani da waya, ba idan muka dubi yadda ake amfani da wadansu kayayyaki wajen sarrafa sako ko kuma shi kanshi wayar sai muga abun kamar sihiri. Mu dauki yadda ake amfani da Bluetooth na zamani wajen amsa waya da kuma yin wadansu al’amura, kama da karbar sakon waya, wanda suka shafi rubutu, ko sauti ko kuma Video da dai makamantansu dukkan su muna iya amfani da Bluetooth wajen sarrafawa. Haka idan kana amfani da Bluetooth na zamani sai kaga cewar zaka iya yin zance na rubutu na kai tsaye (chat) da mutum ba tare da hannunka ya taba jikin handset din kaba. Gashi kuma babu wata harkar joni da waya daga wani abu zuwa jikin wani abu.
Har ila yau ana amfani da Wayar-Tafi-Da-Gidanka wajen shiga Internet wanda ya zamanto shi wani fage ne na musamman a harkar sadarwa. Bayan iya shiga intanet ana kuma iya bude shafukan intanet din, haka kuma idan kana amfani da waya wacce take da WAF ko da karami ne a jikinta zata iya zama wani kundi da zaka iya amfani da shi ya hada ka da intanet din, wato zaka iya mayar da ita a matsayin modem (Abin sadarwa) wanda zaka iya hada ta da computer ta Desktop ko kuma Laptop wajen shiga Internet. saboda haka Wayar-Tafi-Da-Gidanka ta taimaka maka wajen karfin sadarwa.
Wani abu da na ci gaba kuma , shine yadda ake amfani da waya ka kira mutum kana ganinshi yana ganin ka (video-call) wanda za ka iya yin magana da mutum kana ganin shi yana ganinka kamar kuna tare a wuri guda.
Ana amfani da Wayar-Tafi-Da-Gidanka wajen harkar tsaro, ko dai gida, ko kuma abin hawa. Misali ta bangaren abin hawa zaka iya hada wayarka tare da mota ta wajen lura da yanayin da motarka take ciki a inda ka ajiyeta. Misali zaka iya hada kai da daya daga cikin kamfanonin sadarwa kamar MTN ko Etisalat su hada maka layin wayarka tare da abin hawanka, ta yadda idan baka kusa da ita zata fada maka duk abinda ya faru da ita. Ko da kofa aka taba, nan take ba tare da bata lokaci ba zata fada maka, wani abun mamaki ma zata iya gaya maka wace kofa aka taba daga cikin kofofin motar.
Da za ayi rashin sa’a a dauke motar za ta gaya maka a dai-dai inda motar take lokacin da kake nemanta. Ko da yake masu karin magana suna cewa “Duk miyar da tayi dadi, an kashe mata kudi ne”, ya danganta da irin kayan tsaro da kasawa motarka ko kuma daidaitawar da ku ka yi da kamfanonin sadarwan. Domin idan kabiya isashshen kudi za a iya tsayar da motar a inda take.
Daga karshe, ita kanta wayar zaka iya sa mata wani application a cikin ta wanda zai dinga lura da ita kanta wayar ta hanyar amfani da internet, ta yanda in wani ya dauke wayar ya cire SIM din ka ya sa nashi nan take zaka samu sanarwa ta layin abokinka ko wani layin da ka sa idan an canza SIM din wayar a sanar dakai, zata gaya maka SIM din da aka sa, da lokacin da aka sa da kuma wurin da aka s aka. ILLA IYAKA.

No comments:

Post a Comment