Wani ma'aikacin kamfanin Antivirus na Symantec mai suna Shuan Aimoto ya gano cewa App din sunansa "HTML Source Code Viewer" wanda kuma Developers dinsa suna da lakabi da Sanuba Gaming Shi App din yayi kama da Developing Tool wato Tool da ake hada ko gyaran HTML Codd a ciki, amma kuma na karya ne A maganar gaskiya App din yana daukan Videos da Hotuna na wayar mutum ya turasu zuwa Webserver ( " proqnoz.info") wacce anan ne masu App din suke amfani dasu.
Abin fahimta anan shine; Duk lokacin da wani ya mallaki files dinka tofa zai iya amfani dasu wajen kala-kalar salon cuta a Internet.
Wannan ba shine na farko ba domin wata 3 da suka wuce Symantec sun gano wani App mai suna "Beaver Gang Counter" wanda shi kuma sace duk wani files yake wanda yake da alaka da Viber idan kanayin Viber.
A yanzu haka maganar da nake tuni Symantec sun sanarwa da kamfani Google matsalar harma Google din sun cireshi daga Play Store, Sai dai kuma kila ya shafi mutane domin kuwa kafin Google su cireshi anyi Downloading dinsa sau sama da 5000.
Anan abun da mutane ya kamata suyi shine; Ya kamata kafin suyi Downloading din App su tabbatar sun duba Permission dinsa da kuma wanda ya hada App.
No comments:
Post a Comment