yanda zaka hana kamfanonin
sadarwa aiko maka da sakonnin
da bakaso
Hukumar kula da kamfanonin
sadarwa ta kasa -NCC ta
kaddamar da nambobi 2442 da
mutum zai yi amfani dasu wajen
dakatar da duk sakonnin da baya
bukata daga kowane kamfanin
sadarwa da yake amfani dashi.
So tari Jama'a na korafi
sakamakon yadda suke yawan
samun sakonni a wayoyinsu na
tallace-tallace da sauran sakonni
daga kamfanonin sadarwa
wadanda basa bukata.
Lura da wannan tasa hukumar
NCC ta kirkiri gajerun nambobin
2442 wadanda mutum zai yi
amfani dasu domin dakatarwa ko
tace sakonnin da yake so su rika
shigowa wayarsa.
"Ko wane kamfani (Layin
sadarwa) mutum ke amfani dashi
MTN, GLO, Airtel, Etisalat da dai
sauransu. Zai aika sakon “stop
zuwa ga 2442’’ shikenan ya huta
da sakonni mararsa amfani.
YEDDA ZAKA DAKATAR SAKO DAGA KAMFANIN SADARWA
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment