Kasancewar Manhajar nan ta Facebook da ake sanya ma waya, wato Facebook App, a matsayin wata hanya mafi sauki da mutane ke amfani da ita domin shiga dandalin sada zumunta na Facebook, ya sa mutane da yawa kan yi amfani da ita wajen shiga tare da yin Chatting a Facebook.
Amma ba duka daga cikin mutane ba suka fahimci irin matsalolin da wannan app na Facebook ke janyo ma waya da kuma wanda ke amfani wayar.
A cikin wannan kasidar, mun raba wadannan matsaloli zuwa gida biyu, kuma zamu yi sharhi a kan ko wane daga cikinsu.
1. YANDA MATSALAR KE SHAFAR WAYA
******************************************
Matsala ta farko da Facebook App ke haddasa ma waya ita ce, da zaran mutum yayi installing dinsa, zaya rika ja masa data tare da kara girma, abin da kan sanya Memory ya yi saurin cikewa. Abin da ya sa kuma App din yake cike memory shine, yana daukar duk wani hoto, video da kuma rubutu da ka gani a saman Facebook tare da ajiye su a cikin kan memory.
Wannan ne ya sanya idan da zaku duba App din (a cikin App Manager) zaku ga a ko da yaushe girmansa kara karuwa yake yi.
Sanadiyyar wannan nauyi da app din ke karawa,
a wasu lokutan yana sanyawa waya ta rage sauri ( ta koma yin slow), tare da yin tsaye chak (hooking) idan abin ya tsananta.
2.YANDA MATSALAR KE SHAFAR MUTUM
******************************************
Wannan app an tsara shine domin ya janyo hankalin mutane ta yanda zasu rika kashe lokaci mai yawa a saman Facebook din ba tare da sun fita ba. Ku kanku zaku iya fahimtar hakan,
saboda idan kuka kula zaku ga cewa, idan kuna amfani da app din to ba zaku taba ganin karshen posts da mutane ke yi ba.
Wannan na sanya mutum yayi ta mataya kasa (scrolling) ba tare kula da lokacin da ya bata ba.
Wata matsalar kuma ita ce, wannan app na Facebook yana hana mutane fahimtar ma’ana da kuma amfanin Internet.
Wannan na faruwa ne saboda app din an tsara shi ne ta yanda ba zaya taba barin mutum ya shiga wani shafin Internet kai tsaye ta hanyar wannan app din ba.
Wannan ke sanyawa ko da mutum ya so ziyarar wani shafin (ta hanyar link) to sai ya yi ta loading ba tare da ya bude shafin ba. Wannan ne ya sanya wasu mutane da sun ji an ambaci INTERNET,
to tunaninsu baya wuce FACEBOOK. Domin shi kadai suka sani. Alhalin Facebook kuma daya ne daga cikin dubban shafukan da zaku iya samu a saman INTERNET# din.
Shawarar da zamu baku a nan ita ce, in har kuna bukatar kaucewa wadannan matsaloli da muka ambata, to ku rika shiga Facebook ta hanyar Browsers na (kamar Opera, Chrome da dai sauransu) domin su ne zasu baku cikakkiyar damar fahimtar ma’anar Internet da kuma amfaninta wajen ci gaban harkokin yau da kullum.
No comments:
Post a Comment