Menene Ebook
Yaya Ake Amfani Dashi
Ebook ko kuma Littafin Kwamfiyuta (yadda ake kiransa da Hausa) littafi ne amma wanda akayi domin karantawa a computer ko waya ko kuma duk wata na’ura dake da manhajar bude Ebook wato Ebook readers. Yawanci Ebooks sukanzo ne akan tsari (format) na .pdf Littattafan Ebooks na bukatar manhajar Acrobat Reader domin budesu kuma a samu daman karantasu, saboda haka idan kana bukatar karanta littafin kwamfiyuta wato Ebook a kwamfiyutar ka ko kuma a wayarka, to dole saika mallaki daya daga cikin wadannan readers din. Akwai da yawa daga cikin wadannan Readers din wasu na siyarwa ne wasu kuma kyauta ne, Amma wadanda aka fi amfani dasu yanzu haka sune na Adobe Readers. To Yanzu Yaya Za’ayi Na Samu Wannan Manhaja Ta Reader? *.Ga masu amfani da computer, zaku iya downloading din Adobe reader a
DOWNLOAD ANAN *.Ga masu amfani da Wayar Android zaku iya downloading din Adobe Reader a Play Store, kawai kuyi searching. *.Ga masu amfani da BlackBerry kuma kuyi searching din Documents To Go AppWorld *.Ga masu amfani da Nokia sai kuyi searching din Ionic E-Book Readera ovi store. Da Fatan wannan bayanin xai taimaki dalibai da yawa.
Data Kabiru Abdullahi
No comments:
Post a Comment