Akwai hanyoyi guda biyu da za mu yi amfani da su wajen sanya Kwamfuta ta kashe kanta da kanta (automatic shutdown) ;
HANYA TA FARKO 1 :- Ka yi (right click) wato ka taɓa ɓangaren dama na mouse a kan desktop a wajen da ba komai, waɗansu zaɓi za su bayyana sai ka zaɓi (New), bayan ka taɓa new waɗansu zaɓin zai sake fitowa sai ka zaɓi (SHORTCUTS), zai buɗe maka wani shafi akwai wajen rubutu sai ka rubuta (shutdown -s -t 3600) ba tare da wannan baka biyun ba, sai ka taɓa (NEXT) sai kuma ka taɓa (FINISH).
Icon zai bayyana a kan desktop dauke da sunan shutdown sai kai double click a kan sa, shi ke nan ka ba wa kwamfutarka umarni ta kashe kanta a lokacin da ka saka mata.
KARIN BAYANI;- 3600 yana matsayin awa ɗaya a lissafin daƙiƙoƙi domin 60secs × 60mins = 3600secs. Za ka iya amfani da duk adadin mintin ko awa da kake so. Misali ; 900secs = 15mins, 1800= 30mins da dai sauran su .
Yadda Ake Kashe Kwamfuta Aduk Lokacin Da Ka Ke So Batare Da Ka Taɓa Ta Ba (AUTOMATIC SHUTDOWN)
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment