Yadda zaka Bude Email Address Cikin Mintina Qalilan Da Wayar Ka Ko Computer: So dayawa mutane suna tambaya ya zasu bude email ta waya,kuma akwai masu son su shiga abubuwa da dama amma basu da email,to yau ka tsaya ka natsu ka bude email dinka cikin sauki. wasu tambaya suke shin hakan na yiwuwa kuwa? Amsar itace YES... Mene Ne Email? Email wata fasaha ce ta masu irinta, wacce aka bullo da ita dan asan ka da ita kuma ta zame maka makullin shiga gurare da dama a internet, wanda wasu mutane sukan samu matsala musamman idan sunje cika form sai a tambaye su email kaga sun fasa, da email zaka iya tura saqo kuma kaima a turo maka saqo, zaka iya tura hoto har da video duka. kadan kenan daga bayanin email... Ya ake bude email? kafin na amsa wannan tambayar zan lissafo wasu daga cikin sannanun email domains... 1. GMAIL www.gmail.com 2. Yahoo! www.yahoomail.com 3. AOL www.aol.com 4. Hotmail www.hotmail.com 5. msn www.msn.com Wacce ni nafi recommending domin features dinta da sauqi gurin budeta itace google mail wato GMAIL… gmail tana da dadin sha’ani kuma suna baka kyauta 15 Gig a idan ka budeta sabuwa, zaka iya tura saqon sms kyauta ta gmail, kuma duk wanda yayi maka reply zaka samu 5 additonal cikin gmail sms dinka, zaka iya samun text msg a yayin da sabon email ya shigo, zaka iya storing contacts dinka ko kayi importing daga wayar ka, idan kana da bb ka hadata da mail to kwantar da hankalin ka domin nambobin wayan ka na hawa kan gmail suna zama incase ka yarda wayan ko an sace. Infact gmail qarshe ne, kuma ku sani gmail duk wata features ne dake tattare da google, wanda goggle ko ba’a fada ba kasan babba ce a yanar gizo, in Allah ya yarda zanyi bayani akan google… Matakan da zaka bi gurin bude gmail account, 1. Ka tanadi waya ko computer wacce zaka iya hawa internet da ita Idan kana da waya koda nokia C1 ce in har zakayi browsing da ita to zata bude maka email… Da farko>>> ka bude www.gmail.com idan ta bude se kaje create account (with computa or phone). Idan Ta Bude >>> da computa zata nuna maka gurin saka suna, sunan baba, username dinda kake so, shekara, number waya, email din da kake amfani da ita a wannan lokacin (idan baka da email tun dama to ba lallai ne ka saka komai a gurin ba), gurin saka password (password din gmail daga takwas ne zuwa sama, zaka iya saka number dinka yafi sauqin tunawa) sannan zai fito maka da wasu rubutun aljanai wai ka rubuta ka tabbatar masu kai ba robot bane, ka duba da kyau ka rubuta yadda suka rubuta tare da space idan sun saka… kana haka sai kayi marking din accept, kada ka manta dole zaka fada masu ko kai male ne ko female domin susan ko waye kai… idan ka gama wannan duka se kayi next step, zai fito maka da number dinka, sannan yace voice call ko text (abun da suke nufi shine sunaso su kiraka ko su tara maka saqo da wasu nambobi domin verifying account din) sai ka saka number din da za’a iya kiranka da ita ko a tura maka saqo, (in case kace su kira, dan Allah kada su kira kace hello, domin computer ne zata maka Magana, idan kuwa ina kusa google suka kira kace hello ni dariya zanyi maka).. kana saka number din da suka fada maka ko kuma suka turo maka sai kasa continue, shikenan ka gama bude gmail, zasu nuna maka congratulation, can qasa zasu ce your email address is
Kabiruabdullahi632@gmail.com . Shikenan Da Fatan An Gamsu. If You Have Question u are free to ask? Daga:-Kabiru Abdullahi
Yadda zaka Bude Email Address Cikin Mintina Qalilan Da Wayar Ka Ko Computer
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment